BitKova Academy

1.3K posts

BitKova Academy banner
BitKova Academy

BitKova Academy

@BitkovaHub

Empowering learners through our comprehensive crypto education platform. Join us online at https://t.co/6D4VsNWS4v or visit our Kano/Kaduna/Bauchi/Yola Offices.

Gombe, Nigeria انضم Nisan 2021
65 يتبع14.4K المتابعون
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Sunnonin Sallar Eidul Fitr da Yakamata mu sani. Yakai ɗan uwa mai albarka kayi ƙoƙarin domin dacewa da sunnar fiyayyen halitta Annabi Muhammad ﷺ gobe ranar Eidin Sallar Azumi ka lizimci waɗannan abubuwan domin samun ladar koyi da Annabi Muhammad ﷺ, gasu kamar hakan: 1⃣Wanka Domin Sallar Eid (الموطأ للإمام مالک 432) 2⃣ Sanya turare, Sanya Tufafi masu kyau. (المطالب العالیة 1:85) 3⃣Cin Abinci kafin Zuwa Sallar Eidi (Eidil Fitr) ( صحیح البخاری 953) 4⃣Tafiya Kasa Zuwa Eidi (530 سنن الترمذی) 5⃣ Sauraron Khudubah bayan gama Sallar Eidi ( صحیح سنن ابن ماجه1073 ) 6⃣Chanza Hanya yayin dawowa daga Sallar Eidi (صحیح البخاری 986) 7⃣ Addu'o'in yayin Haduwa da mutane " تقبل الله منا و منکم" (مسند الإمام أحمد) 8⃣ Nuna farin ciki da Nishadi (صحیح مسلم) Domin samun lada daga Allah kuyi, tagging da retweeting ɗinsa domin ƴan uwa su amfana. Allah ya karɓa mana. Rubutawa da gabatarwa ©️ Engr Aliyu Almustapha (@aliy_almustapha)
BitKova Academy tweet media
Català
0
2
21
279
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Yanzu haka ana kan Registration na ajin 2026 har zuwa ranar Asabar, 28th March, daga nan za a rufe domin shirye-shiryen fara karatu. Ranar fara karatu zai kasance Asabar, 4th April, Insha Allah. Idan kana son koyon Crypto Trading da yaren Hausa cikin sauki kuma yadda zaka fahimta, wannan babbar damace gare ka. Karku bari lokaci ya wuce muku. Domin yin register, garzaya shafin mu: bitkova.com
BitKova Academy tweet mediaBitKova Academy tweet mediaBitKova Academy tweet mediaBitKova Academy tweet media
Indonesia
2
0
22
888
BitKova Academy أُعيد تغريده
Mahmoud Sardauna | Aptos Educator
Mahmoud Sardauna | Aptos Educator@Mahmoudsardauna·
Bro-to-Bro A monetized account on X is worth more than $10k cash. You can literally make money!
English
78
23
285
4.7K
BitKova Academy أُعيد تغريده
Mahmoud Sardauna | Aptos Educator
Mahmoud Sardauna | Aptos Educator@Mahmoudsardauna·
Saka attachment Haram! Askin rabin kai da gashi, rabi babu gashi ga maza shima Haram. Muje maha 🚶🏃
हिन्दी
40
20
220
3.5K
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Ramadan Reminder| Day 25 Manzon Allah ﷺ ya ce: Azumi da Al-Qur’ani za su yi ceto ga bawa a Ranar Alƙiyama. Azumi zai ce: “Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha’awa da rana, ka ba ni izinin in yi masa ceto.” Al-Qur’ani kuma zai ce: “Ya Ubangiji! Na hana shi barci da dare saboda yana karantani, ka ba ni izinin in yi masa ceto.” Sai Allah Ya ba su izinin su yi masa ceton. (Sahih Jam'i 3882) Ma’ana a takaice: Wannan hadisin yana nuna cewa azumi da karatun Al-Qur’ani ibadu ne masu girman lada, har ma za su tsaya su kare mutum a Ranar Alƙiyama. Darussa daga hadisin: Azumi ibada ce da za ta yi ceto ga mutum a lahira. Karatun Al-Qur’ani musamman a Ramadan yana da babbar lada. Hada azumi da karatun Al-Qur’ani yana daga cikin manyan ayyukan Ramadan. Allah ya sa azuminmu da karatun Al-Qur’aninmu su zama dalilin cetonmu a Ranar Alƙiyama. Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌍bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
2
0
15
242
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Ramadan Reminder | Day 24 Manzon Allah ﷺ ya ce: Allah Ya ƙasƙantar da mutumin da Ramadan ya zo masa, sannan watan ya wuce bai samu gafarar Allah ba. (Sunan al-Tirmidhi 3545) Ma’anar Hadisin: Ramadan wata ne na rahama da gafara. Allah yana ba bayinsa dama su tuba, su ƙara ibada, su nemi gafara. Idan mutum ya samu wannan wata amma bai yi anfani da shi ba, wannan babban hasara ne gare shi. Darussa daga hadisin: 1️⃣ Ramadan babbar dama ce ta neman gafarar Allah. 2️⃣ Kada mu yi sakaci da ibada, sallah, Qur’ani, azumi da addu’a a watan Ramadan 3️⃣ Lokaci yana wucewa da sauri, don haka a yi anfani da Ramadan kafin ya ƙare. 4️⃣ Babbar hasara ne mutum ya rasa gafara a wannan wata mai albarka. Allah Ya sa mu dace da samun gafararSa a Ramadan. Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌍bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
1
1
15
260
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Allah ya karɓi ibadunmu yasa muna cikin mutanen da za'a ƴanta daga wuta zuwa aljanna a cikin wannan wata mai albarka. Shigo Bitkova Academy domin samun ingantaccen ilimin zamani da gogewa daga ƙwararrun Malamai. 🌍bitkova.com/our-hub Bitkova Academy, Makarantar ku, abin alfaharinku
BitKova Academy tweet media
Indonesia
2
0
21
423
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Ramadan Reminder | Day 23 An karɓo daga Ibn Abbas (RA) ya ce: Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyauta a cikin mutane. Kuma yakan fi yawan kyauta a watan Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu yake zuwa wajensa. Jibrilu yana zuwa wajensa kowace dare a Ramadan, suna karanta Al-Qur’ani tare. Saboda haka Manzon Allah ﷺ ya fi iska mai gudu wajen yawaita alheri da kyauta. Sahih Bukhari hadith mai lamba ta 3554 Ma’anar Hadisin: Hadisin yana nuna cewa kusanci da Al-Qur’ani da yawaita ibada yana ƙara wa mutum son yin alheri da taimakon mutane. Shi ya sa Manzon Allah ﷺ yake ƙara karamci sosai a Ramadan. Darussa daga Hadisin: Ramadan lokaci ne na ƙara sadaka da taimako ga mutane. Karatun Al-Qur’ani yana gyara zuciya kuma yana ƙara son alheri. Ya kamata mu koyi karamci da halin Manzon Allah ﷺ musamman a wannan wata. Allah ya sa mu zama masu yawan alheri a Ramadan. 🤲 Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌍bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
3
1
16
229
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Ramadan Reminder| Day 22 Daga Abdullah ibn Umar (Allah Ya yarda da su duka) ya ce: “Manzon Allah ﷺ yana yin ’itakafi a cikin kwanaki goman ƙarshe na Ramadan.” Ma’anar hadisin a taƙaice: Ikaaf shine zama a masallaci don tsarkake lokaci daga duk abin duniya, yin ibada, addu’a, karatun Alƙur’ani, da tunani game da Allah. Darussa 3 daga wannan hadisi: 1. Muhimmancin kwanaki goma na ƙarshe: Wannan hadisi yana nuna cewa Manzon Allah ﷺ yana mai da hankali sosai a cikin kwanaki goma na ƙarshe, domin samun lada da kusantar Allah. 2. Tsarkake lokaci don Allah: Yin ikaaf yana koya mana yadda mu ware lokaci na musamman don ibada, nesa da duniya da damuwarta. 3. Ilimi da ibada tare: Ta hanyar kasancewa cikin ikaaf, mutum yana ƙara karatun Alƙur’ani, addu’a, da tsarkake zuciya, wanda yake ƙarfafa dangantaka da Allah. Allah Ya sa mu dace da wannan lada a cikin kwanaki goma na ƙarshe. Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌎bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
0
0
12
223
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Ramadan Reminder | Day 21 Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya shiga kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, yana ƙara ƙaimi wajen ibada, yana tsarkake kansa, yana tashi da dare yana yin ibada, kuma yana tashe iyalinsa su yi ibada tare da shi.” Bukhari ne ya ruwaito shi Bukhari 2024. Ma’ana a taƙaice: Lokacin kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, Manzon Allah ﷺ yana ƙoƙari sosai wajen tsarkake zuciya da jiki, yana tashi dare yana salla da addu’a, kuma yana ƙarfafa iyalinsa su yi haka tare da shi. Wannan yana nuna mana muhimmancin ƙoƙari da himma a cikin kwanaki goma na ƙarshe. Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌎 bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
1
0
6
237
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Ramadan Reminder| Day 20 Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya ce: “Ku nemi Lailatul Qadri a dararen witiri (21, 23, 25, 27, 29) na kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan.” Bukhari ne ya ruwaito shi. Bukhari 2017 Ma’ana a taƙaice: Manzon Allah ﷺ yana umartar mu da mu yi ƙoƙari sosai wajen neman Lailatul Qadri, musamman a dararen witiri daga cikin kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, domin a can ne mafi yawan yiwuwar samun ta. Allah Ya ba mu dacewa da cin ribar wannan dare mai albarka. Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌎bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
1
0
11
191
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
New Week. New Goals. New Purposes. New Mindset. Domin gina gobenka mai inganci, shigo makarantar Bitkova Academy. Muna koyar da courses masu kayatarwa da ake buƙata a duniya. Ka koya yau, ka samu a gobe! Tsarin koyi, ka samu zai baka damar koyon skills cikin ƙanƙanin lokaci, kuma ka fara samun kuɗin shiga daga abin da ka koya. Shigo Bitkova Academy, shigo koyi, ka samu. Bitkova Academy, Makarantar ku, abin alfaharinku. 💙 Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A 🌍bitkova.com/our-hub
BitKova Academy tweet media
Indonesia
1
1
20
285
BitKova Academy
BitKova Academy@BitkovaHub·
Inna lillahi wa inna ilaihi Raji'oon Mun samu labarin rasuwar ɗaya daga cikin yara marayun da suka halarci Bitkova Academy – Orphanage Summer Kids Programme a Gombe. Yaron ya kasance mai ƙoƙari sosai, mai hazaƙa da kaifin basira, mai saurin fahimtar karatu da kuma hardacewa. Irin wannan hali nasa ya sanya ya zama abin alfahari ga malamai da abokan karatunsa. Muna roƙon Allah (SWT) Ya sanya rasuwarsa ta zama rahama ga iyayensa, Ya kuma sanya shi cikin yara ƙanana da suke ƙarƙashin kulawar Annabi Ibrahim (AS) Allah Ya gafarta masa, Ya ba iyayensa da iyalansa haƙurin jure wannan ƙaddara. A madadin Bitkova Academy, muna miƙa sakon ta’aziyya ga iyayensa, da ɗaukacin Al’ummar Musulmi kan wannan babban rashi.
BitKova Academy tweet media
Indonesia
18
2
87
2.9K