SMARTCRYPTOBOI 📉💵@AminuAm91202
Ba wai kana rashin girma a X ba ne...
Kana ɓata lokacinka ne ba tare da tsari ba.
Ka taɓa lura?
Wasu suna shafe awa 6 zuwa 8 suna scrolling, suna replies, suna neman engagement...
Amma ba sa ɗaukar ko awa ɗaya suna koyo ko inganta kansu.
Wannan shi ne babban kuskure.
Idan duk abin da kake yi shi ne kallon abin da wasu suke yi, ba za ka taɓa zama abin kallo ba.
Ka fara amfani da lokacinka cikin hikima:
• Ka ware lokaci don koyo.
• Ka yi bincike kan masu nasara a niche ɗinka.
• Ka tsara post ɗinka kafin ka wallafa.
• Ka yi engagement da manufa, ba don kashe lokaci ba.
• Ka ƙayyade lokacin da za ka yi amfani dashi a X.
• Ka duba irin posts ɗin da suka yi kyau, ka koyi darasi daga gare su.
• Ka huta idan ka gaji domin kada ka gaji da tafiyar.
Ka tuna:
Ba yawan awannin da ka shafe a X ne ke sa account ya girma ba.
Yadda ka yi amfani da waɗannan awannin ne ke kawo ci gaba.
Kada ka kasance mai yawan Hawa online kawai.
Kasance mai ƙirƙirar abin da mutane za su tsaya su karanta.
Kai fa, kana amfani da X ne don gina makomarka, ko don kashe lokaci? 👇