ALMADANEE DIGITAL AND GLOBAL CONCEPTS LIMITED retweetledi

Masu skills irin na Professor Isa Ali Pantami a kamfanin Google, Microsoft, Amazon da Binance tamu ta crypto duk shekara ana biyansu daga $300,000 zuwa $450,000, Wato daga Naira Million 411, Zuwa Million 616.
Wannan salary kenan banda stock bonus na kamfani. Ana kiran skill din Chief Information Security Officer, Wato shugaban dake kula da bangaren Cybersecurity, Irin wannan aikin Malam ya yiwa Nigeria a 2023.
Sannan Irinsu malam dai sune AI Research Scientist, Wadanda duk shekara suna samun salary a shekara daga $250k zuwa $650k Wato daga 342 Million zuwa 930 Million Naira, Haka ake biyan wadanda suke aiki a AI Mind, Microsoft d.s.s.
A bangaren consultantation da malam babban kamfani ne dashi a Abuja a wannan bangaren, bincike ya tabbatar da Cybersecurity consultants suna iya samun abinda bai gaza $300k ba a shekara, Wato dama 400 Million Naira. Banda sauran ayyukan da suke yiwa Gwamnati kamfanoni a kasashen Duniya.
Skill irin na Cybersecurity, AI Research da Technology Consulting suna daga cikin ayyukan da ake biya mafi tsada a duniya saboda suna da matukar muhimmanci ga tsaron bayanai da cigaban fasaha.
Idan mutum ya kai matakin da kamfanonin duniya kamar Google, Microsoft, Amazon ko Binance suke nema, samun manyan kudade ba abin mamaki bane.
A maimakon mutane su rika mamakin arzikin masu ilmi, ya kamata mu fara girmama knowledge economy da value na expertise. A wannan zamanin, ilmi da skill sun fi yawancin albarkatu daraja.
Irin wadannan mutanen kake tambaya ina suka samu 90 Million Naira? 🤣🤣🤣 Dan Allah bakaji kunya ba? 🤔
Wannan fa kadan ne daga cikin skills biyu kacal na lissafo wanda malam yake dasu wanda ga abinda masu su suke samu a duniya. Banda sauran harkokin business dinshi da yake gudanarwa.
Rubutawa Uthman Khan

Indonesia






















