Trust Radio Live
5.3K posts

Trust Radio Live
@TrustRadioLive
Official X page of Trust Radio 92.7FM Abuja, Nigeria...The voice you can Trust. Listen to us live on our website for your up to date news and entertainment. RT
FCT - Abuja Katılım Şubat 2023
109 Takip Edilen475 Takipçiler

Jami'an tsaro na DSS sun cafke wata matashiya, Nafisa Usman, mai shekara 25 wadda ake zargi da ƙwarewa wajen safarar harsasai tsakanin jihohi a Kano.
Jami'an sun yi nasarar cafke wadda ake zargin ne a ɗaya daga cikin manyan tashoshin motocin Kano, bayan ta sayo harsashai tare da ɓoye su cikin buhunan garin gero da shinkafa daga Jihar Nasarawa, domin kai su Kankara a Jihar Katsina.
DSS ta bayyana cewa ta wacce ake zargi ne yayin wani samame da aka kai bayan samun sahihan bayanai.

Indonesia

Rahotanni daga birnin Jos na Jihar Filato na bayyana cewa sabon rikici ya barke a garin tun bayan saukaka dokar hana fita da gwamnatin ta saka bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Angwan Rukuba inda aƙalla mutane 28 suka mutu tare da raunata wasu da dama.
Wakilin Aminiya ya tabbatar da cewa wasu ɓata-gari sun kai hare-hare kan direbobi da masu wucewa a wurare daban-daban na birnin, lamarin da ya sake jefa jama’a cikin fargaba.

Indonesia

Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kaduna ta ɗage sauraren buƙatar neman beli da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya shigar zuwa ranar 14 ga Afrilu.
A yayin zaman kotun lauyan El-Rufai, Iyamu Oyewole, ya jaddada cewa beli hakki ne na kundin tsarin mulki.
Sai dai ɓangaren masu tuhuma sun buƙaci kotu ta ki amincewa da belin, suna masu cewa akwai yiwuwar El-Rufai ya yi tasiri ga shaidu ko kuma ya hana ci gaban bincike idan aka sake shi.

Indonesia






















