Aminiya

46.8K posts

Aminiya banner
Aminiya

Aminiya

@aminiyatrust

Sahihin Shafin Jaridar Aminiya. Jaridar Hausa Ta Rukunin Kamfanin Media Trust; Mamallakin Jaridar Daily Trust, Trust TV Da Kuma Trust Radio.

Abuja, Nigeria Katılım Temmuz 2014
468 Takip Edilen105.4K Takipçiler
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
ICPC ta saki El-Rufai bayan rasuwar mahaifiyarsa Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa da ke tsare da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta sallame shi domin halartar jana’izar mahaifiyarsa. Wannan na cikin wani saƙo da ɗansa, Bashir El-Rufai, ya fitar a daren Juma’a a shafinsa na X.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
2
124
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam, ya yi murabus daga muƙaminsa. Sanarwar da mai magana da yawun Kwankwasiyya ya fitar ta ce ya ɗauki matakin ne domin kare zaman lafiya da daidaiton mulki a jihar. Tun da farko, Majalisar Dokokin Kano ta fara shirin tsige shi, kuma kotu ta ƙi dakatar da shirin. Sai dai an bayyana cewa murabus ɗin ba ya nufin ya amince da zarge-zargen da ake masa ba, yana mai jaddada cewa bai aikata laifin komai ba.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
4
152
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai ya sanar da rasuwar kakarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ita ce mahaifiyar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bello ya bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne a ‘yan sa’o’i kaɗan da suka gabata. Ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai daraja wadda ta yi rayuwa mai cike da albarka da tarbiyya. Bello ya ƙara da cewa iyalan suna godiya ga irin rayuwar da ta yi, tare da roƙon Allah Ya gafarta mata, Ya kuma jiƙanta.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
11
243
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi baƙuncin Sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Abuja. Kwankwaso ya tabbatar da ganawar, sai dai bai yi cikakken bayani kan abin da suka tattauna ba. Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin tattaunawar yiwuwar haɗakar siyasa tsakanin ƙungiyar Kwankwasiyya, jam’iyyar ADC da kuma NDC gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin irin wannan ganawa na iya zama wata alama ta yunƙurin kafa sabuwar haɗaka, wadda za ta iya sauya fasalin siyasar Najeriya a gaba.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
9
251
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Gwamna Abdullahi Sule ya gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a birnin Makkah yayin gudanar da Umrah. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya tsagwaronta, yana mai cewa babu wata ganawa da ta gudana tsakanin gwamnan da Atiku. Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Sule bai taɓa yin wata ganawa da Atiku ba a Makkah, tare da jaddada cewa raɗe-raɗin ganawar a matsayin na yaudarar jama’a. Haka kuma, gwamnatin ta sake nanata cikakken goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa irin waɗannan rahotanni ba za su sauya matsayarta ta siyasa ba.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
1
217
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Aminiya tweet media
ZXX
2
0
1
158
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta tanadi sama da mayaƙa miliyan ɗaya domin yiwuwar faɗa da Amurka, yayin da tashin hankali ke ci gaba da ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa an ɗauki wannan mataki ne a matsayin shirin ko-ta-kwana, idan rikicin ya rikide zuwa yaƙin ƙasa. Sai dai har yanzu babu tabbacin yadda lamarin zai ɓarke, yayin da ake ci gaba da fargabar ƙarin tsanantar rikici a yankin.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
5
263
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Wata mata mai suna Hafsatu Yusuf ta haifi jarirai biyar (maza uku da mata biyu) a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano. Mijinta, Malam Salisu Nafiu, ya ce matarsa ta sauka lafiya, kuma da ita da jariran duk suna cikin ƙoshin lafiya. Ya kuma bayyana cewa wannan ita ce haihuwarta ta tara. Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ɗauki nauyin kula da lafiyar uwa da jariran.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
9
247
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
A yanzu kwana nawa N10,000 take yi maka kafin ta ƙare?
Aminiya tweet media
Indonesia
6
1
8
605
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyar ADC saboda ba ta da abin da za ta iya bayarwa. Shettima ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a filin baje kolin kasuwanci da ke birnin Gusau a Jihar Zamfara, inda ya kwatanta jam’iyyar da “ƙashi babu komai.” A cewarsa, ADC ba ta da ƙarfin da ake buƙata domin magance matsalolin ’yan Najeriya, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ba ta da wani amfani ga jama’a. Ya kuma ƙara da cewa jam’iyyar na fama da rashin ingantaccen tsari da manufofi da za su iya kawo ci gaba a ƙasar.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
6
257
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Wani mummunan harin kwantan-bauna da ’yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar akalla sojoji tara da dan sanda guda a Karamar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ce lamarin ya faru ne da daren Talata a kauyen Giro Masa, inda jami’an tsaron suka fada tarkon ’yan ta’adda. Mazauna yankin sun ce an kona motocin sojoji guda biyu yayin harin, wanda suka bayyana cewa ya jefa al’umma cikin firgici, ganin yadda kwanciyar hankalin al’umma ya qara dagulewa. aminiya.ng/yan-bindiga-su…
Aminiya tweet media
Indonesia
0
2
5
261
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Biyo bayan yunƙurin tattaunawa da Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci dakarun ƙasar da su dakatar da duk wasu sabbin hare-haren da ake shirin kai wa cibiyoyin makamashi na Iran. Rahotanni sun nuna cewa matakin ya shafi hare-haren kan muhimman cibiyoyin makamashi ne na tsawon kwanaki biyar, domin bai wa tattaunawar damar ci gaba. Shugaban ya bayyana cewa hakan zai buɗe ƙofa da yiwuwar cimma yarjejeniya da za ta kai ga tsagaita wuta a rikicin da aka shafe sama da makonni uku ana gwabzawa tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda, da Iran a ɗaya ɓangaren. Sai dai duk da iƙirarin da Amurka ke yi na cewa ana tattaunawa, Iran ta musanta hakan. A halin yanzu, rikicin na ci gaba da haifar da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, duk da ƙoƙarin wasu ƙasashe na shiga tsakani domin samar da zaman lafiya.
Indonesia
0
2
4
164
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Tsakanin mace mai tsafta amma ba ta da haƙuri, da mai haƙuri amma ba tsafta wacce ta fi sauƙin zama?
Aminiya tweet media
Indonesia
7
0
15
466
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Yadda wata babbar mota ta yi haɗari a daidai ƙofar shiga gidan gwamnatin Jihar Gombe Hoto: Oyekachukwu Obi
Aminiya tweet mediaAminiya tweet mediaAminiya tweet mediaAminiya tweet media
Indonesia
0
0
5
346
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Kalli yadda Iran ta yi luguden wuta kan wata Unguwa a Isra'ila Hoto: Fb/Aljazeera
Aminiya tweet mediaAminiya tweet mediaAminiya tweet mediaAminiya tweet media
Filipino
0
0
7
220
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta yi watsi da buƙatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, bayan da aka gurfanar da shi a gabanta a ranar Talata. Lauyoyinsa sun buƙaci kotun da ta ba shi beli, amma lauyoyin Hukumar Yaƙi da Rashawa ta ICPC da ke ƙarar sa, sun buƙaci a ci gaba da tsare shi. A cewar lauyoyin na ICPC, zarge-zargen da ake yi masa na da nauyi, kuma bayar da shi beli na iya kawo tsaiko ga binciken da suke ci gaba da gudanarwa. Daga ƙarshe, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Maris na wannan shekara.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
5
155
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Me za ku iya faɗi kan wannan shiga ta Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a wani taron APC a Jihar Adamawa?
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
5
254
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi ƙarin bayani kan dalilin da ya sa yake tunanin tsayawa takarar kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawa a zaɓen shekarar 2027. Gwamnan a baya ya ce ba shi da burin ko buƙatar neman kujerar Sanata bayan kammala mulkinsa, amma a yanzu ya ce matsin lamba da yake fuskanta daga iyayensa da magoya baya ya sa dole ya sake tunani a kai a yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Litinin.
Aminiya tweet media
Indonesia
1
0
2
245
Aminiya
Aminiya@aminiyatrust·
Rahotanni kafafen yaɗa labarai na Gabas ta Tsakiya syn rawaito cewa ƙasar Iran na ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami zuwa wasu biranen ƙasar Isra'ila a daren yau Talata. Jaridar Roya ta rawaito cewa, Isra'ila ta kakkaɓo wasu makamai masu linzamin da aka harba zuwa birnin Nagev. Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya a daren ya nuna yadda makaman Iran ke sauka ba tare da kariyar Iron Dome ta Isra’ila ta tare su ba a yankin Ramat Gan na Tel Aviv.
Aminiya tweet media
Indonesia
0
0
5
187