Sabitlenmiş Tweet

Part 1️⃣
Yadda Ake Amfani da Sentiment Analysis Don Sanin Ko Token Zai Yi Tashi Ko A’a✍️
Da farko Ku taimaka kuyi like, retweet and bookmark domin wasu su gani su amfana.
Sentiment analysis yana taimakawa wajen fahimtar yadda mutane suke ji game da kasuwa, wanda zai iya taimakawa wajen sanin ko wani token zai tashi ko kuma zai fadi. A DEX trading, fahimtar yanayin kasuwa yana da matukar muhimmanci domin zai taimaka maka ka zabi coin mai kyau kafin ya fara tashi.
A cikin wannan rubutun, za mu koyi: ✔ Yadda ake duba sentiment na kasuwa ✔ Yadda ake amfani da Twitter da Telegram wajen tantance token
1️⃣ Yadda Ake Duba Sentiment na Kasuwa
Kafin ka saya wani token, yana da kyau ka bincika yadda mutane suke jin dadin wannan token. Ga wasu hanyoyi da zaka iya amfani da su wajen duba sentiment:
✅ Dexscreener Trending: Idan token yana cikin jerin trending tokens, yana iya nuna cewa mutane suna sha'awar sa. ✅ Crypto Twitter: Duba hashtags ko ko akwai masu tasiri da suka yi magana game da token. ✅ Telegram Group: Idan mutane suna magana da kyau game da token da kuma devs suna aiki da gaske, wannan yana nuni da kyau.
2️⃣ Yadda Ake Amfani da Twitter da Telegram Wajen Tantance Token
👉 Twitter (X)
1️⃣ Je zuwa search bar na Twitter.
2️⃣ Rubuta sunan token ko contract address.
3️⃣ Duba abinda mutane ke cewa game da token.
4️⃣ Idan manyan influencers ko DEX TRADERS suna magana akansa, to token da yuwuwar ya tashi.
👉 Telegram
1️⃣ Shiga cikin official group na token.
2️⃣ Duba ko devs suna aiki da gaske ko suna ƙoƙarin tallata token kawai.
3️⃣ Idan mutane suna magana akan rug pull ko scam, wannan yana nufin ka guji token ɗin.
To be continued...✍️

Indonesia


























