Sabitlenmiş Tweet

Fundamental Analysis part six (6)Marketing and Branding
Marketing and Branding na nufin kuɗin da wani project ya ware domin tallata coin ɗinsa da kuma sa mutane su san shi. Wannan shine marketing and branding
Misali Kayi tunanin an bude sabon shago a unguwarku, Idan ba a yi talla ba mutane ba za su san akwai shagon ba.
Haka ma coin yake. Idan ba a tallata shi ba mutane kaɗan ne za su saya ko su yi amfani da shi.
Saboda haka masu ƙirƙirar coin kan ware wani kaso daga cikin kuɗin da za a samu domin
~Tallata coin a kafafen sada zumunta.
~Haɗa kai da manyan influencers.
~Sanya coin a manyan kasuwannin crypto (Exchanges).
~Gina suna da amincewar jama'a.
Misali
Idan an samar da coin 10,000,000 ana iya ware 2,000,000 ko kuma kuɗin da aka samu daga sayar da wannan kaso domin gudanar da talla da bunƙasa sunan project ɗin.
Wani zai tambaya me yasa wannan yake da muhimmanci wajan Fundamentalanalysis?
~Mutane da yawa za su san coin ɗin.
~Masu saya za su ƙaru.
~Mabukata zasu ƙaru, wanda zai iya taimakawa farashin coin ya haɓaka.
Amma idan ba a ware isasshen kuɗi domin marketing ba ko da coin ɗin yana da kyakkyawar manufa, yana iya kasa samun karɓuwa saboda mutane ba su san da shi ba.
Darasin anan shine Kafin ka saka kuɗinka a wani coin yakamata ka duba ko project ɗin ya ware isasshen kasafi domin Marketing and Branding, domin talla mai kyau na daga cikin manyan abubuwan da ke taimakawa nasarar coin.
Shine kana duba yanayin yadda project yabawa bangaren marketing and branding mahimmanci wajan bincike kafin ka saka kudi ??
#cryptocurrency #cryptoedu

Filipino



























